Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Jarida Ya Kasance Min Hanya Mafi Sauki Da Zan Wa'azantar -Inji Khadija Mai Atampa


Na kasance marubuciya, inda nake aika sakon ilmantarwa tare da fadakarwa, daga bisani na lura da cewar hanya mafi sauki da zan wa’azantar ita ce hanyar aikin jarida inji malama Khadija Tijjani Mai Atampa.

Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA,

Malama Khadija ta ce ta karanci kwas din Islamic studies bayan ta kammala ne ta nemi gurbin karatu a kwalejin Sa’adatu Rimi, ta kuma karanci aikin jarida.

Malama Khadija ta kara da cewa bata fuskanci wata matsala ba kasancewar dama ita marubuciya ce don haka, isar da sako ta hanyar jarida ya zo mata da sauki.

Khadija, ta ce bayan kammala karatunta sai da ta dauki ‘yan lokuta kafin ta samu aiki, kuma babban abin sha’awa a aikin da take shine ta fadakar ta hanyar daukar wata matsala da take ciwa al’umma tuwo a kwarya.

Daga karshe ta ja hankali matasa da su jajirce wajen neman ilimi domin magancewa kansu matsloli zaman duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG