Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ASUU Ta Janye Yajin Aiki


Shugabannin kungiyar ASUU tare da shugaban Majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila yayin wani zaman sulhu da majalisar ta shirya don kawo karshen yajin aiki
Shugabannin kungiyar ASUU tare da shugaban Majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila yayin wani zaman sulhu da majalisar ta shirya don kawo karshen yajin aiki

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu mambobin kungiyar ta ASUU suka shiga yajin aikin kan neman a biya su wasu hakkokinsu tare da inganta fannin ilimin jami’o’i a duk fadin kasar.

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU, ta janye yajin aikin wata takwas da ta kwashe tana yi.

Rahotanni sun ce, kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan wani taro da shugabanninta suka gudanar daga daren Alhamis zuwa wayewar garin Juma’a inda aka yanke shawarar malaman su koma bakin aiki.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ASUU ta shiga yajin aikin kan neman a biya su wasu hakkokinsu tare da inganta fannin ilimin jami’o’i a duk fadin kasar.

Manyan kafafen yada labarai da dama a Najeriyar sun ruwaito wani jami’i a cikin kwamitin zartarwar kungiyar ta ASUU, wanda ya tabbatar da cewa sun janye yajin aikin ne bisa sharadi, ko da yake jami’in ya nemi a sakaya sunansa.

Jami’in ya kara da cewa, nan ba da jimawa ba, shugabanninsu za su fitar da sanarwa a hukumance.

Shugabannin kungiyar a matakan jihohi sun kira taro ne a sakatariyar ASUU da ke Abuja, babban birnin Najeriya don tattauna hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, wanda ya umarce su su koma bakin aiki.

Kotun daukaka karar ta nemi malaman su janye yajin aikin kafin ta saurari karar da suka shigar.

XS
SM
MD
LG