Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ASUU: Gwamnatin Tarayya Ta Janye Umarnin Da Ta Ba Shugabannin Jami’o’in Kasar


Taron majalisar zartarwa a Najeriya (Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)
Taron majalisar zartarwa a Najeriya (Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)

Sai dai hukumar ta NUC, ba ta bayyana dalilinta na janye wannan umarni da ta bayar ba.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi amai ta lashe bayan da ta janye umarnin da ta ba shugabannin jami’o’in kasar da su bude makarantu.

A ranar Litinin hukumar da ke kula da jami’o’in kasar ta NUC, ta ba shugabannin jami’o’in wato Vice Chancellors, Pro-Chancellors da sauran masu gudanarwa, umarnin su bude jami’o’in kasar.

Tun a watan Fabrairun wannan shekara malaman jami’o’in na Najeriya suka shiga yajin aiki kan wasu bukatu da suka hada da sabunta yarjejeniyar da ke tsakanin malaman jami’a karkashin kungiyarsu ta ASUU da gwamnatuin tarayya, baya ga bukatar da suka mika ta neman a yi wa jami’o’in kasar gyare-gyare.

Sai dai kamar yadda rahoton suka nuna, sa’o’i bayan ba da wannan umarni, hukumar ta NUC, ta aike da wata sabuwar sanarwa wacce ke nuna cewa ta janye wannan umarnin na farko.

“An ba ni umarnin na janye wannan sanarwa mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/135, mai kwanan wata 23 ga watan Satumba, 2022.” Sanarwar mai dauke da sa hannun Darektan kula da kudaden hukumar ta NUC, Sam Onazi ta ce kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

Hukumar ta NUC ba ta bayyana dalilinta na janye wannan umarni ba.

Wannan lamari na umarnin na NUC na faruwa ne yayin da rikicin bangarorin biyu yake kai-komo a kotu.

A ranar 21 ga watan Satumba, kotun ma’aikata da ke Abuja, ta umarci kungiyar malamai ta ASUU da ta janye yajin aikinta.

A karshen makon da ya gabata ASUU ta kalubalanci hukuncin Alkali Polycarp Hamman, inda ta daukaka kara.

Tun da farko gwamnatin tarayya ce ta shigar da ASUU kara inda ta nemi kotun ta ba malaman jami’ar umarnin su koma bakin aiki.

Gabanin a kai ga zuwa kotu, bangarorin biyu sun yi zama a lokuta daban-daban don neman maslaha amma abin ya gagara.

.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG