Kwamishinan lafiya, Dr. Olaokun Soyinka, ya bada wannana shawara a taron da ma’aikatar lafiaya ta shirya, tare da hadin guiwar kungiyar Reckit Benckinser, yayin bukin ranar yaki da zazzabin cizon sauro ta duniya.
Soyinka yace, wannan zai samu ne idan iyayen suna sa yaransu su kwana a karkashin gidan su kuma lura da kewayensu. Bisa ga cewarshi, sauro ba zai iya haduwa ba idan muhalli da tsabta.
A cikin nashi bayani, shugaban Reckit Benckinser, Mr. Ashok Bhashin yace, kungiyarsa na shirye ta hada hannu da gwamnati domin shawo kan cutar zazzabin cizon sauro.