ABUJA, NIGERIA - Akwai matukar bukatar daukar matakan kawo wa irin wadannan yara daukin da zai ceto rayuwarsu ta nan gaba. Za a iya cimma wannan buri ne ta hanyar gudunmawa asusun raya ilimi da tallafi daga hukumomin taimako.
Bincike ya nuna cewa akwai fiye da yara miliyan 10 da ke gallafiri a titunan Arewacin kasar ba tare da samun ilimi ko damar shiga makaranta ba. Tsarin hada makarantun tsangaya da na boko zai yi matukar tasiri wajen magance wannan kalubalen.
Shiga shafin a saurari cikakken rahoton: