Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Tana Zargin PDP da Horas da 'Yan Bangan Siysa a Jihar Gombe


APC
APC

A jihar Gombe jam'iyyar APC shiga wani takunsaka da jam'yyar PDP mai mulkin jihar

Jam'iyyar adawa ta APC tana zargin PDP da shirin horas da matasa 2000 domin 2015.

APC ta ce gwamnatin jihar Gombe ta dauki matasan 2000 da za'a ba horo irin na soji domin a yi anfani dasu a matsayin 'yan bangan siyasa lokacin zabukan 2015. Shugaban riko na jam'iyyar APC a jihar Barrister Magaji Dohu shi ya yi ikirarin hakan cikin firar da yayi da wakilin Murya Amurka. Yace "Sun dauki mataki wanda suke ganin in sun bi shi ne zai sa su ci zabe inda suke son su horas da matasa su basu horon sojoji kamar mutane dubu biyu"

Wakilin Muryar Amurka ya tambayi Barrister Dohu ko gwamnatin tarayya ce ta sa aka dauki mutanen ko kuma jihar Gombe ce take son ta samu nata sojojin. Sai yace "Wannan jihar Gombe ce keyi inda ta nemi tsoffin sojoji da 'yansanda su zo su bada horo wanda ma sun nemi izini a ma'akatar tsaro wato ministry of defence amma labarin da ya zo wurinmu basu samu approval su yi wannan ba"

An tambayeshi ko akwai barazana ne horas da matasan? Sai yace "Siyasa yaki ne. Siyasa yaki ne amma da kuri'a a keyinta" Dangane da ko ita jihar ko zata yi anfani da matasan ne wajen siyasa sai Barrister Dohu yace "Ko a yanzu ma an fara anfani da wadanda suka riga suka samu horo".

Wakilin Muryar Amurka ya sake tambaya ko lokacin da aka dauki matasan ita gwamnati ta fada zata yi anfani dasu a fannin siyasa. Yace kowa ya san siyasar arewa. Za'a kashe mutane ne a cimma buri.

Kan matakan da suka dauka Barrister Dohu yace "Muna rokon addu'a a masallatai da mijami'ai Allah ya kawar da mummunan aniyar PDP a Najeriya"

To sai dai kwamishanan matasa na jihar Gombe Alhaji Mijinyawa Sani Labaran da yake mayarda martani kan zargin na APC yace ba haka ba ne. Ya cigaba da cewa "Maigirma gwaman jihar Gombe Dr Ibrahim Hassan Dankwambo idan ka tuna a baya musamman lokacin da ya karbi jagorancin wannan jiha ya tabbatar zai inganta rayuwar matasa shi ne aka fito da wannan shiri aka yi na mutum 1200 a Malam Sidi a 2012 san nan aka sake daukan 330 aka kaisu Jos Shere Hills kuma duk mutum mai son jihar Gombe ya ga irin gudunmawar da mutanen ke bayarwa. Kan siyasa za'a iya fadan komi. Ba'a yi a baya ba ne? An dinga yi ne contiuous abu ne"

Gwamnatin Gombe a nata bayanin ta ce ta kaiwa majalisar dokokin jihar wadda ta yi dokar amincewa. A tsarin aikinsu ba zasu musgunawa kowa ba. Haka kuma basa daukan makami ko dorina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG