Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC: An Yi Wa Amina Zakari Takwarar Aiki a Ghana


Shugaba Mahama na Ghana
Shugaba Mahama na Ghana

Bukin ranstar da sabuwar shugabar hukumar zabe a Ghana Mrs. Charlotte Osei a fadar shugaban kasa ya sha ban-ban da abunda aka saba gani, saboda wannan ne karo na farko da kasar ta ranstar da mace a matsayin shugabar hukumar zabe.

Wannan buki ya samu hallartar shuwagabannin jam’iyyun siyasa na kasar.

Da yake rantsar da ita, shugaban kasa John Dramani Mahama ya ambato gogewa da tayi a fanni daban-daban inda ya kyautata mata zaton yin wannan aikin.

Sai dai shugaban ya tunatar da Mrs. Osei yace wannan babban aiki ne, da aka dora miki, don haka ya zama wajibi kiyi aiki tukuru kamar yadda jama’ar kasar suke hasashe.

Shugaba Mahama ya cigaba da yin bayani inda ya yabawa tsohon shugaban hukumar zabe mai barin gado yana cewa “Dr. Kuji Afarajad ya tabbatar wa kasar nan gogewarsa tsakanin shekaru 20 wajen tsara shirye-shiryen zabe da gudanar da zaben. Ya ce duk da irin korafi da muke a matsayin mu na ‘yan siyasa, a cikin gwamnati ko ‘yan hamayya”.

A nata bangare, sabuwar shugabar hukumar Mrs. Osei tayi alkawari tana cewa “da gudunmuwar sauran ma’aikata na hukumar zata yi kokari ta cigaba da karfafa hukumar domin ta iya yin aiki babu sani, babu sabo.”

Kafin wannan mukami Charlotte itace shugabar hukumar wayar da al-ummar kasa akan hakkokinsu da wajibobinsu ga kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG