Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Ma Tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ‘Daurin Talala


A combination of file pictures made on May 27, 2015 shows Fifa officials (LtoR, from upper row) Rafael Esquivel, Nicolas Leoz, Jeffrey Webb, Jack Warner, Eduardo Li, Eugenio Figueredo and Jose Maria Marin
A combination of file pictures made on May 27, 2015 shows Fifa officials (LtoR, from upper row) Rafael Esquivel, Nicolas Leoz, Jeffrey Webb, Jack Warner, Eduardo Li, Eugenio Figueredo and Jose Maria Marin

Wani alkali a kasar Paraguay yace an yi daurin talala ma tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kasashen Nahiyar Amurka ta Kudu, a yayin da ake ci gaba da binciken abubuwan fallasa da suka danganci zarmiya da cin hanci a hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA.

Shi dai Nicolas Leoz, mai shekaru 86 da haihuwa, yana kwance a asibiti a Asuncion, babban birnin kasar Paraguay, ana masa jinyar hawan jini, amma an shirya sallamarsa zuwa gida tun jiya da maraice.

Leoz yana daya daga cikin manyan jami’an kwallon kafar duniya, tsoffi da wadanda har yanzu suke kan kujerunsu, da ake bincike game da batun zarmiya da cin hanci a hukumar FIFA.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Paraguay, ta samu takarda daga ofishin jakadancin Amurka ta neman a kama Leoz a kuma mika shi ga Amurka.

Lauyansa, Fernando Barriocanal yace Leoz yana cikin yanayi na kwarin guiwa kuma a shirye yake ya kare kansa idan lokacin yin hakan yazo.

Leoz shine shugaban hukumar kwallon kafa ta kasashen nahiyar Amurka ta kudu, wadda aka fi sani da lakanin CONMEBOL, daga 1986 har zuwa 2013.

XS
SM
MD
LG