Kwamanda Christian Ezekobe kakakin sojojin ruwan Najeriya yace daga watan Janairu zuwa na Afirilun wannan shekarar an samu aika aikar masu fashi da makami a kan teku har sau ashirin da biyar da kuma ta'adancin 'yan yankin Niger Delta.
Sintirin da suka yi ya taimaka wajen dakile ayyukan miyagun mutane akan teku da kuma kare kamfanonin man fetur dake yankin. Babban hafsan sojojin ne ya kirkiro da shirin sintirin domin a tabbatar da lafiyar mutane da dukiyoyi ta kawar da bata gari dake kan teku.
Shirin sintirin na farko ya kare ne a watan Yuni. Kana aka yi na biyu da ya dauki kwanaki sittin ana gwagwatawa da bata gari. Yanzu da shiri na biyu ya kare sai kuma na ukku.
Kwamanda Ezekobe yace tunda aka kaddamar da kashi na biyu ba'a samu fashi da makami a kan teku ba koda ma sau daya. Yace da yaddar Allah zasu yi kokari su cigaba da dakile aikace aikacen 'yan tsagera.
Wani Abubakar Abdulsalam kwararre a sha'anin ruwa yayi tsokaci akan wannan shirin na ukku. Yace sintirin ba zai samu nasara ba sai an samu hadin kan wasu kasashe da suke cikin kungiyar tsare tekun. Yace misali idan 'yan tsagera sun yi barna a yankin Najeriya da zara sun tsere zuwa yankin wata kasar a kan teku to ba za'a iya kamasu ba sai da hadin kai da yaddar mahukuntar kasar. Akwai iyakokin kasashe aka kowane teku.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.