Hukumar hana fasa kwauri ta kasa a Najeriya wato Customs, ta fara raba kayayyakin abinci da aka kama daga masu shigo da shi ba bisa ka'ida ba zuwa cikin kasar.
Hukumar ta ce ta fara rarraba kayan abinci kamar shinkafa, man girki, da sabulu ga ‘yan gudun hijira da marayu, da kuma wasu mabukata.
Bayan rabon kayan, a jihar Rivers, an nuna damuwa ga yadda aka tafiyar da wannan rabon kayan, don ana zargin cewar akwai cuwa-cuwa a wajen harkar raba kayayyakin ga ‘yan gudun hijira, inda wasu jami’ai sukan hada baki don karkata kayan abincin, saboda biyan wasu bukatunsu.
Wakilin Muryar Amurka ya yi magana da wasu a wajen rabon kayayyakin, inda suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda aka yi rabon.
Sai dai jami'in hukumar ta Custom da ya jagoranci wannan shiri na raba kayayyaki, Yakubu Salihu, ya musanta cewa an yi wani abu da ba daidai ba.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Abubakar Lamido Sakkwato.
Facebook Forum