An yi imanin wadanda aka kashen karuwai ne kuma wanda ake zargin ya zuwa yanzu yana fuskantar tuhuma daya na kisan kai.
An kama shi ne a ranar Lahadin da ta gabata dangane da bacewar mace daya amma kuma an gano wasu gawarwaki biyar yayin da aka kama shi.
Ana sa ran wanda ake zargin zai kasance cikin jerin mutanen da aka kama kafin ya sake bayyana a gaban kotu a ranar 18 ga watan Oktoba, a cewar jami'ai.
Lamarin ya janyo cece-kuce daga kungiyoyin kare hakkin mata da ke kira ga ‘yan sanda da jami’ai da su kara kaimi wajen yaki da cin zarafin mata.
Kungiyoyin sun yi zanga-zanga a gaban kotun majistare ta Johannesburg yau Talata, inda suka yi kira da a hana wanda ake zargin beli.
An hana kafafen yada labarai buga hotunan wanda ake zargin har sai an fitar da jerin sunayen wadanda ake zargin.