Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'ar Borno na Murnar Nasarar Sojoji


Yayin da sojojin Nijeriya ke ta ikirarin yin nasarar kwato wurare da dama daga 'yan Boko Haram, 'yan Niijeriya na ta bayyana ra'ayoyinsu.

Yau kimanin kwanaki goma kenan da jami’an tsaron Nijerliya su ke ikirarin sake kwato wuraren da ‘yan Boko Haram su ka kwace daga hukumomin Nijeriya. Kuma dattawan jihar Borno sun kira taron manema labarai a Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, inda suka nuna farin cikinsu da likirarin hukumomin tsaron Nijeriya. To amma sun kuma yi kira ga jami’an tsaron da su rinka gayyatar ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki zuwa irin wadannan wuraren don su gane wa idonsu su tabbatar da abin da ke wakana.

Wakilinmu a Maiduguri Haruna Dauda, ya ce duk da yake babu wani dan jaridar da yaje ya gane ma kansa ikirarin sake kwato wuraren da jami’an tsaro ke yi, jama’a na cigaba da bayyana farin cikinsu. Haruna yace an yi ta nuna hotunan wasu motocin soji da ‘yan Boko Haram su ka sace, da kuma hotunan wasu da aka ce ‘yan Boko Haram ne da su ka yi shigar mata don su samu su sulale ganin wutar da su ke sha daga sojojin Nijeriya.

Haruna ya kuma ruwaito wasu daga cikin mazauna jihar ta Borno na bayyana farin cikinsu da dangane da nasarar da jami’an tsaron Nijeriya ke ikirarin samu. To saidai wasunsu na jefa ayar tambaya kana bin da ya sa aka kasa samun nasara a baya sai a wannan lokaci.

Jama'ar Borno na Murnar Nasarar Sojoji - 3'10"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG