Ana sa ran akalla yan kasar Afrika ta kudu dubu 14 zasu hallara a Johannesburg a filin wasan cricket a yau talata domin jin bayanai da tsohon shugaban Amurka Barack Obama zai gabatar a daren ranar bikin cika shekaru 100 na haihuwar marigayin nan dan gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata Nelson Mandela.
A na sa ran Obama zai karfafawa matsan Afirika ta kudu guiwa, su ci gaba da gwagwarmayar da Mandela ya dade yana yi domin ci gaban demokradiya, banbancin launin fata, ‘yancin dan adam a lokacin gabatar da kasida da aka sabawa gudanarwa shekara shekara, ta Nelson Mandela a karo na 16. Wannan jawabin shine babban taron da shugaba Obama zai gabatar tun barin shi fadar white house a shekarar 2017 bayan yayi shekaru 8 akan mulki.
An kulle Mandela a kurkuru har tsawon shekaru 27 a karkashin dokar Afirika ta kudu ta farar fata mai tsauri kafin a sake shi a shekarar alif dari tara da casa'in, ya kuma zama shugaban bakar fata na farko bayan shekara 4 a zaben kasar na kabilu daban daban na farko.
Facebook Forum