Yayin da ake fama da annobar cutar korona, ana kan sake jan daga a wani dadadden wurin mai cike da sarkakkiyar siyasa, yayin da jiragen yakin ruwan Amurka da China ke yawaita sintiri a Tekun Kudancin China.
“A wannan satin Amurka ta gudanar da atisayen jaddada ‘yancin zirga-zirgar a tekun Kudncin China har sau biyu. Jiragen yakin ruwan Amurka na USS Barry da USS Bunker Hill duk sun fara atisaye su ka kuma kammala a wuraren da mu ka ga dama, kamar yadda mu ka saba,” a cewar mai magana da yawun Hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon, Jonathan Hoffman ga manema labarai jiya Jumma’a.
USS Bunker Hill, mai dauke da makami mai linzami wanda aka girke a Yammacin tekun Pacific, ya yi sintiti ranar Laraba a ruwayen da ke daura da tsibirin Spratly Islands wadanda China da wasu kasashen ke ikirarin mallakinsu ne. Shi kuma USS Barry mai ruguza makami mai linzami ranar Talata ya danna cikin ruwayen da ke daura da tsibirin Paracel Island, wadanda kasashen China da Vietnam da Taiwan kowacce ke ikirarin na ta ne.
Facebook Forum