Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Juyayin Mutuwar Solomon Lar


Solomon Lar
Solomon Lar

Bayan da aka sanarda mutuwar Chief Solomon Lar a jihar Filato jama'a sun shiga juyayi.

Rasuwar da duk al'ummar jihar Filato ke kira babansu ya kada jihar domin yadda ya rikesu ya kuma gudanar da harkokin jihar a lokacin da yake mulki.

An bayyana Chief Solomon Doshep Lar tsohon gwamnan farar hula na farko a jihar Filato a matsayin mutumin da ya sadakar da kansa wajen bautawa Allah da yin hidima ma jama'arsa iyakacin rayuwarsa. Duk da cewa matarsa da 'ya'yansa basa gidansa a Jos domin suna tare da shi a wurin jinya aAmurka amma da aka sanarda rasuwarsa nan da na gidan ya cika makil da mutane. An tarar da mutane suna ta kuka suna juyayin rashin da aka yi. Wata da ta yi magana a madadin dangi ta ce baba ya dauki nauyin dangi da ma wadanda ba dangi lokacin da yake raye.A cewarta babu wanda ya zo neman taimako wurinsa da ya tafi hannu banza. Gargadin kwana kwanan nan da ya yiwa 'yanuwansa shi ne na hada kai da tabbatar da zaman lafiya.

Chief Solomon Lar ya rike mukamai da dama. Shi ya fara zama gwamnan farar hula na farko a jihar Filato a shekarar 1979 a karkashin jam'iyyar NPP. Ya kuma zama shugaban PDP na farko a Najeriya. Yayin da yake gwamnan Filato ya habaka harkokin ilimi inda ya gina manyan makarantu guda 100 a Filato da Nasarawa wadda a lokacin tana hade da Filato. A bangaren kiwon lafiya ya gina asibitoci 23 wanda da ya cika da magunguna da ma'aikata. kana ya mayarda asibitocin da gwamnati ta kwace ga masu su. Haka ma ya yi aiki kan samarda ruwan sha ma jama'a da hanyoyi da wutar lantarki da gina kasuwar da babu irinta a duk fadin Afirka. A gwamnatin tarayya kuma ya rike mukamai da dama wadanda suka hada da shugabancin kwamitin rikicin jihar Filato a shekarar 2010.

Ambassador Yahaya Kwande ya yi abokantaka ta kud-da-kud da marigayi Solomon Lar.Ya ce shugaba ne na anihi. Ko yana gwamnati ko baya gwamnati shugaba ne. Ya ce mutum ne wanda yake bukatar ya rika bayarwa. Lokacin da yake gwamna an samu zaman lafiya. Babu wani rikici na kowane iri. Ya rike Musulmi da Krista ko a cikin gidansa ma. Haka ma ya rike 'yan siyasa da nashi da na ;yan hamayya. Ya dauki nauyin duk mutanen Filato. Ya ce ba karya ba ne ake kiransa baba lar.

Zainab Babaji nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG