Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gudanar Da Babban Zabe a Kasar Jamus


Zaben Jamus
Zaben Jamus

Al’ummar kasar Jamus zasu gudanar da babban zabe yau da zai yanke hukunci kan ko Angela Merkel zata yi tarihi wajen samun yin wa’adin na hudu a matsayin shugabar gwamnati.

Binciken ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a jajiberin zaben ya nuna Jam’iyar Merkel Christian Democratic Union da Christian Social Union, suna kan hanyar samun gagarumar nasara. Ana kyautata zaton jam’iyun biyu zasu sami tsakanin kashi talatin da shida zuwa talatin da tara na kuri’un da za kada.

Yayin da jam’iya mafi girma ta biyu a kasar Jamus, Social Democrats wadanda suka dan dafawa gwamnatin Merkel da wa’adinta ya cika, mai yiwuwa ta sami kashi ishirin da uku cikin dari na kuri’un kawai, da idan haka ta tabbata, zai kasance sakamakon zabe mafi muni da jam’iyar ta samu tun shekara ta dubu biyu da tara.

Masu harsashe kan harkokin zabe sunce jam’iyar masu ra’ayin rikau AFD-zata iya samun kashi biyar cikin dari na kuri’un da suke bukata su sami kujeru, abinda basu samu ba a zaben shekara taq dubu biyu da goma sha uku. Masu sharhi kan lamura da dama suna harsashen cewa, AFD na iya samun kashi goma cikin dari na kuri’un da zai basu kujeru sittin a majalisa, wannan zai maida it jam’iya ta uku mafi girma a majalisa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG