A yau Litinin za a ba ‘yan majalisar wakilai masu shigar da kara a shari’ar tsige shugaban Amurka Donald Trump, da rukunin masu kare shugaban sa’o’i biyu-biyu domin rufe mahawarar da suke yi.
Da alama an gama samun sakamakon shari’ar, inda 'yan jam'iyyar Republican ke da rinjaye da mambobi 53 a kan 'yan Democrats mai mambobi 47 a majalisar dattawan, babu wanda ya nuna wata alama a cikinsu akan cewa zai goyi bayan a tsige Shugaba Trump.
‘Yan Democrats a majalisar wakilan za su ci gaba da caccakar Trump, akan yin amfani da matsayinsa ba bisa ka’ida ba a lokacin da ya bukaci Ukraine ta gudanar da binciken da zai taimaka masa a siyasance, da kuma yin shisshigi a harkokin majalisa.
'Yan majalisar su na kuma zarginsa da hana jami’an gwamnatinsa ba da bayanai da kuma bayyana a matsayin shaidu a lokacin binciken.
Majalisar ta dattawa, ta kuma yi watsi da batun kiran shaidu, lamarin da bai yi wa ‘yan Democrat dadi ba.
Sanata Tom Carper, dan Jam’iyyar Democrat a Majalisar Dattawan ya ce, “Ta yi wu, a ce shugaban ya yi nasara, amma cikin kwanaki masu zuwa, za su fadi karara idan gaskiya ta bayyana.”
Lauyoyin Trump da ma shugaban kansa, sun hakikance kan cewa bai aikata laifi ba, dan haka abin da ya yi bai kai a tsige shi ba.
Facebook Forum