Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fuskantar Karancin Guraban Aiki A Kasashe Masu Tasowa - ILO


Tambarin Kungiyar Kwadago Ta Duniya.
Tambarin Kungiyar Kwadago Ta Duniya.

Hauhawar farashin kayayyaki a duniya da yawan basussuka da yakin Ukraine, da kuma jinkirin murmurewa daga annobar COVID-19 sun sa kasashe masu tasowa fuskantar karancin guraben aikin yi don tallafa wa al'ummarsu, in ji wani rahoto daga kungiyar. Kungiyar Kwadago ta Duniya ko ILO a takaice.

A rahotan hukumar ILO kan ayyuka ta gano cewa yawan ayyukan yi a yawancin kasashe masu tasowa ba su koma kan matakin da suke ba kafin annobar COVID-19, kamar yadda su ma manyan kasashe irinsu Amurka ke fuskantar karancin ma’aikata da hauhawar albashi.

"Binciken wannan rahoto ya kasance abin tunatarwa ne game da karuwar rashin daidaito a duniya," in ji Darakta Janar na ILO Gilbert F. Houngbo a cikin wata sanarwa.

Houngbo ya yi kira da a hada hannun jari na kasa da kasa wajen samar da ayyukan yi a kasashe masu tasowa, ta hanyar kokarin da hukumar ILO ta kira hadin gwiwar duniya don adalci na zamantakewa.

"Saka hannun jari ga mutane ta hanyar ayyukan yi da kariyar zamantakewa zai taimaka wajen rage tazarar da ke tsakanin kasashe masu arziki da matalauta," in ji shi. “Kungiyar za ta hada dimbin kungiyoyi da masu ruwa da tsaki. Zai taimaka wajen sanya adalci na zamantakewa a matsayin ginshikin farfadowar duniya, da kuma sanya shi fifiko ga manufofi da ayyuka na kasashe da yankunan duniya."

Bisa kididdigar da hukumar ILO ta fitar, rashin aikin yi ya yi kamari a Afirka da kuma kasashen Larabawa da dama wadanda, bisa kididdigar da hukumar ta yi, za su kasance kasa da matakin da ake kafin barkewar annoba a kalla har zuwa karshen shekarar 2023.

XS
SM
MD
LG