Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba da Zaman Dar-dar Tsakanin Amurka da Turkiya


Ofishin Jakadancin Amurka dake Ankara, Turkiya
Ofishin Jakadancin Amurka dake Ankara, Turkiya

Takaddamar da ta kunno kai tsakanin Amurka da Turkiya na habaka inda yanzu kasashen biyu na zaman dar dar da juna kuma duniya na fargabar in lamarin ya ci gaba har na wani tsawon lokaci yana iya haifar da illa mai muni

Ana ci gaba da zaman ‘dar-‘dar tsakanin Amurka da Turkiyya, inda Tukiyya ta dakatar da baiwa yawancin Amurkawa visa, domin ramuwar gayya kan makamancin abin da Amurkar ta yiwa kasar.

Sai dai ramuwar gayyar ta soma jefa harkokin kasuwancin Turkiyya cikin wani hali, abinda ake fargabar zai iya haifar da illa mai muni ta wani lokaci mai tsawo.

Da yake gargadi kan wannan abu dake faruwa, masanin kimiyyar siyasa Cengiz Aktar ya ce, “wannan wani abu ne da ba a taba gani ba, koda kuwa lokacinda kasashen suka sami sabanin da ya fi haka muni, ba a taba ganin an shiga irin wannan halin ba, lamarin ba abin wasa bane.”

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Jayayyar dai ta samo asali ne tun makon da ya gabata lokacin da aka kama wani ma’aikacin ofishin jakadancin Amurka mai suna Metin Topuz, ana tuhumarsa da laifin ta’addanci. Lauyoyin Turkiyya sun zargi Topuz da alaka da babban malamin nan da yanzu haka ke zaune a Amurka, Fethullah Gulen, wanda aka zarga da laifin kitsa makircin juyin mulkin da bai samu nasara ba a shekarar da ta gabata.

A jiya Litinin ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta gayyaci mataimakin babban shugaban ofishin jakadancin Amurka inda aka bukaci Amurka da ta dakatar da matakin da ta dauka na hanawa ‘yan Turkiyya visa.

Akwai alamun za a ci gaba da samun zaman ‘dar-‘dar tsakanin kasashen biyu, bayan da ofishin lauyan gwamnatin Turkiya ya bayyana sake karbo izinin kama wani ma’aikacin ofishin jakadancin Amurka dake Istanbul, kuma jami’an tsaro sun rike matar ma’aikacin da ake son kamawa da ‘dansa.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG