Yayin da jama'a ke kokawa game da annobar cutar coronavirus wadda ke hallaka jama'a a fadin duniya, yanzu haka wata matsala da ke tasowa ita ce ta batun cin zarafi da kuma karbar na goro da ake zargin jami'an tsaro da kuma wasu ma'aikatan kotun tafi da gidanka ke yi, musamman akan iyakokin jihohi.
Bincike na nuni da cewa yanzu haka jami'an tsaron da ke kan hanya sun maida shingayen da suka kafa tamkar shago, inda matafiya da direbobi kan bada kudade masu yawa kafin su wuce, kuma da wuya ka yi tafiyar minti biyar zuwa goma ba tare da samun shingen jami'an tsaron ba.
Yanzu haka kudin mota ya yi tashin gwauron zabi sakamakon dokokin da aka kafa.
DSP Suleiman Yahya Nguroje, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ya shaida wa wakilin muryar Amurka cewa, rundunar ‘yan sanda ba ta da masaniyar hakan na faruwa, amma za su gudanar da bincike, kuma duk wanda aka kama da aikata irin wannan laifin daga cikin jami’an ‘yan sanda, to za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Ita ma dai rundunar ‘yan sandan jihar Taraba a ta bakin kakakinta DSP David Misal, ya shaida wa wakilin muryar Amurka cewa, basu da masaniya akan batun amma zasu gudanar da bincike game da wannan zargi da ake yi wa jami’an ‘yan sanda.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Ibrahim Abdul'Aziz.
Facebook Forum