Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Iran Da Kai Hari Kan Tankokin Mai A Tekun Oman


Rundunar sojojin ruwan Amurka ta fitar da wani hotan bidiyo dake nuna wani jirgin ruwan Iran yana dauke da wasu na’urorin da basu fashe ba a jikin ‘daya daga cikin tankokin Man da aka kaiwa hari a tekun Oman.

‘Daya daga cikin tankunan mallakar kasar Norway ne, sauran kuma na kasar Japan ne.

Na’urar tana jikin tankar kasar Japan, tana gaba kadan daga ‘dayar na’urar da ta fashe,Tankar kasar Norway ta kama da wuta, inda hayakinta ya turnuke sararin samaniya wanda za a iya hangowa daga tauraron dan Adam dake sama.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi Iran da laifin kai harin, wanda ya faru a gabar tekun Iran.

Ya kuma ce, wannan hare haren rashin Imanin yana nuna barazana karara ga zaman lafiya da tsaro a duniya, kuma hari ne kan yancin zirga-zirga, lamarin da ba za a amince da barazanar da kasar Iran ke neman haddasawa.

Amma shi kuma Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif, yace wannan harin da aka kai na baya bayanan, akwai alamomin tambaya, domin kuwa Firai Ministan Japan Shinzo Abbey, yana kasar Iran lokacin da suke tattaunawa da wani babban jami’in kasar Ayatollah Ali Khameini a Tehran,domin neman hanyar da za a sasanta tsakanin Amurka da Iran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG