Maharban sun gamu da ajalinsu ne a kyauyen kayamla dake karamar hukumar Jerry a jahar Borno, lokacin da su ke bin wasu da ake zaton 'yayan kungiyar Boko haram ne wandanda ake zaton sun sato wasu shanu.
Maharban sun bi ta kan wani bom da aka dana ne mai karfin gaske da ya tarwatse, ya yi sanadin kashe bakwai daga cikinsu yayinda wadansu tara suka ji mummunan rauni, wadanda suke jinya a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri a halin yanzu.
Tunda farko dai sai da wadansu maharban su ka taka wani bom a kan yanyarsu zuwa Kayamla inda bom din ya fasa masu taya guda amma bai ji wa kowa rauni ba, suka kuma nemi taimako domin sake taya da ta lalace, maharban da suka gamu da ajalinsu sun kai masu dauki ne bayan sake tayar suna kan hanyarsu ta komawa, suka taka wani bom mai karfi da ya zama ajalinsu.
Wani maharbi da Muryar Amurka ta yi hira da shi, ya bayyana cewa, mutanen da suke kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun labe bayan dasa bom din da ya yi sanadin fashewar tayarsu suka jira wucewar motar da ta kai wa ta farko dauki kafin suka dana wani bom suka sake nokewa.
Kungiyar Boko Haram dai ta saba kai irin wadannan hare hare ta gudu ba tare da an kama wani daga cikinsu ba, lamarin da ke ci gaba da barazana ga komawa rayuwa ta yau da kullum a jihar.
Saurari cikakken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u ya aiko daga Maiduguri