Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Shelar Ganin Watan Sallah A Najeriya


Fitowar Wata
Fitowar Wata

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli Akan Al'amuran Musulunci, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.

A wani jawabi da ya yi ta kafafen yada labarai daga fadar sa da ke Sokoto, Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya fara da gode wa Allah (SWA) da ya kawo mu wannan rana ta Alhamis 29 ga watan Ramadan, 1444, wato 20 ga watan Afrilu, 2023, inda ta zamo rana ta karshen azumin watan Ramadan na wannan shekara.

Ya ce sun samu labaru da rahotanni daga shugabanni daban-daban, musamman Malamai a duk fadin kasar na tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal kuma sun karbi wannan rahoto sun gamsu bayan an tattauna an dudduba cewa hakika wannan watan ya tsaya.

Ya kara da cewa bisa ga haka ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023, ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1444, kuma ranar Sallah karama; saboda haka suna kira ga jama’ar Musulmi da su ajiye azumi su yi niyyar zuwa masallaci domin yin sallar idi a wurare daban-daban.

Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Ya kuma yi addu’ar Allah ya karbi dukkan ibadu da aka yi a cikin wannan wata mai alfarma. Har ila yau ya yi wa Najeriya Addu’ar zaman lafiya da kuma rokon Allah ya taimaki zababbun shugabannin da aka zaba a kasar kwanaki da suka wuce.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da suka kara kyautata ayyukansu a kan hanyoyin da addinin musulunci ya umarce su da su zauna lafiya da ‘yan uwansu ba tare da nuna banbanci kabila ko addini ba.

Yanzu dai Najeriya za ta bi sahun wasu kasashen Musulmin duniya na yi sallah karama a ranar Juma’a.

Saurari cikakken bayanin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG