Wata sanarwa da hukumar dake sa ido kan amfani da makamai masu guba ta kasa da kasa ta fitar (OPCW) a yau Juma'a, ta tabbatar da cewa a binciken da ta gudanar, ta gano an yi amfani da makamin Sarin mai guba a farmakin da aka kai ranar 4 ga watan Afirilu a garin Khan Shaykhun dake Syria.
Da yake Magana kan lamarin, shugaban cibiyar, Ahmet Uzumcu, ya ce “Da kakkausar murya na yi Allah wadai da wannan harin rashin imanin, wanda ya sabawa tsarin yarjejeniyar makamai masu guba.
Ya kara da cewa "kuma dole ne duk masu hannu a wannan mummuman aiki a tabatta a hukuntar da su kan abinda suka aikata.”
Ana sa ran cewa binciken hadin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da hukumar ta OPCW zai yi kokarin gano ko su waye suke da hannu a harin, wanda ya yi sanadiyar asaran rayukan mutane 87, ciki har da kananan yara da mata.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka a wata sanarwa da ta fitar ta nuna cikakken goyon bayanta ga binciken da ake gudanarwa.
Facebook Forum