An bada ruhoton cewa an sami kwayar HIV a cikin jikin “marasa lafiya na Boston”, kamar yadda ake kiransu, - maza guda biyu wadanda aka musanya masu bargo wanda yayi kamar ya warkar da su daga cutar kanjamau. Yanzu sun koma ga shan maganin kanjamau.
Sai dai kuma, masana sun ce wannan koma bayan zai bada damar wani mahimman ci gaba cikin binciken maganin da zai kai ga warkarwa.
Yayinda yake magana akan al’amarin, Steven Deeks, Farfesa kan cutar kanjamau da masani a Jami’ar California, San Francisco yace, “Hakika wannan koma baya ne ga marasa lafiyan, amma ci gaba ne ga wannan sashi domin sashin ya sami karin ilimi,”
Deeks da sauran masana suna cewa daya daga cikin abubuwan da wannan ya ke koyarwa shine, kayan gwaje gwajen da aka sa san suna gano cewa akwai kwayar cutar kome kankantarta basu biya bukata ba.
Hade da kwayar cutar HIV, dukan wadannan marasa lafiyan na Boston su biyu suna dauke da wata irin cutar kansa da ake kira lymphoma wadda aka yi masu maganinta ta wajen musanya bargon su – daya a shekara ta 2008 daya kuma a 2010.
Sun cigaba da shan wannan magani na cutar kanjamau, amma bayan marasa lafiyan sun yi wata takwas suna shan magani, likitoci sun bincike su ba tare da sun ga kwayoyin HIV a cikin jinin su ba.
A farkon shekara ta 2013, dukan marasa lafiyan biyu suka yanke shawarar dena shan maganin kanjamau, kuma dukansu suka nuna alamar warkewa – wanda ya sa likitocinsu, Timothy Henrich da Daniel Kuritzkes daga Boston Brigham da Asibitin mata, su baiyyana a wani taro a watan Yuli cewa mai yiwuwa sun warke.
Sai dai kuma, a watan Disamba sai labari ya fita cewa wani daya daga cikin marasa lafiyar ya fara nuna alamun kwayar cutar ta kanjamau tun watan Agusta, bayan da mara lafiya na biyu ya nuna alamar a watan Nuwamba.
Henrich yace, dawowar kwayar na nuna irin gwanintar da HIV ke da shi na boyewa a cikin jiki domin gujiwa hari daga garkuwar jiki da kuma magani.
“Ta wannan binciken mun gano cewa wurin boyewar cutar ta kanjamau yana da zurfi kwarai fiye da yadda aka sani yanzu, kuma ya nuna cewa matakan da kuma kwarewarmu na binciko kwayar cutar sun kasa kwarai,” ya ci gaba da cewa, dukan marasa lafiyan suna “cikin koshin lafiya sosai” kuma sun koma shan maganinsu.