Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Ma'aikatan Kwantar da Tarzoma na Majalisar Dinkin Duniya daga Sudan ta Kudu


Sojojin Sudan ta Kudu dake fafatawa da 'yan tawaye
Sojojin Sudan ta Kudu dake fafatawa da 'yan tawaye

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa an saki ma’aikatanta na kwantar da tarzoma guda 20 da ‘yan tawayen Kudancin Sudan suka kama, amma har yanzu ana rike da wasu ‘yan kwangilarsu guda 12.

Kakakin majalisar Stephane Dujarric yace, an kama ma’aikatan kwantar da tarzomar ne a ranar Litinin a lokacin da suke raka tawagar da ke dauke da man fetur a daidai tekun Nilu.

An tare tarragon dake dauke da man ne a hanyarsa ta zuwa arewacin birnin Malakal, inda daruruwan ‘yan tawaye dauke da makamai suka datse shi a hanya. Suka sace man dake cikinsa sannan suka yi garkuwa da ma’aikatan.

Mista Dujarric yace, a halin yanzu sun kwashe ma’aikatan guda 20 a jirgi mai saukar ungulu daga birnin Kaka zuwa Malakal a jiya Alhamis, amma ma’aikatan kwanturagin hukumar guda 12 suna hannun ‘yan tawayen.

Tawagar wanzan da zaman lafiyar sun damu matuka da rashin sako ma’aikatan tarragon man da shi kansa taragon ba a dawo da shi ba balle kayan ayyukansa.

Kakakin yayi kira ga shugaban ‘yan tawayen Riek Machar ya yi riko da goyawa MDD baya tare da sako wadannan mutane lami lafiya.

XS
SM
MD
LG