Lamarin garkuwa da mutane domin kudin fansa ya sake dawowa gadan-gadan a yankin Niger-Delta mai arzikin Mai. A ‘yan kwanakin nan ne aka sace wasu manyan ma’aikatan kamfanin Mai na Shell a jihar Rivers.
Sai gashi wasu ‘yan bindigar sun sake yin awon gaba da wasu Turawa biyu, dake aiki a kamfanin tace Mai na Niger Delta Petroleum Resources da ake kira NDEP a takaice a garin Abua.
‘Yan bindigar dai sun kutsa ne cikin surku a yankin da ya ratsa ta cikin kamfanin NDEP, inda nan take su ka yi gaba da ma’aikatan kamfanin biyu.
Rundunar gamayyar tsaro ta JTF dake aikin tsaro a yankin Niger Delta, Operation Delta Safe, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda mai magana da yawun rundunar Manjo Ibrahim Abdullahi, ya ce bayan da suka sami labari, sun bi sahun ‘yan bidigar sai dai basu yi nasara ba, amma suna nan suna ci gaba da kokarin ganin sun ceto ma’aikatan.
Haka kuma rundunar JTF ta baiwa kamfanin shawarar ya samar da tsaro a inda yake gudanar da aikinsa, domin kare ma’aikata da kuma dukiya.
Ko a makon da ya gabata sai da aka yi garkuwa da wasu ma’aikatan kamfanin Mai na Shell, a jihar Rivers inda har ya zuwa yanzu babu labarin halin da suke ciki, sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta ce a tsaye take don ganin an ceto su.
Domin karin bayani saurari rahotan Lamido Abubakar.
Facebook Forum