Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin jihar Kaduna Ta Kafa Dokar Hana Fita A Kajuru


Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i yayin da yake jawabi ga wadanda ya kai jaje
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i yayin da yake jawabi ga wadanda ya kai jaje

Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa dokar hana \fita ba dare ba rana a Kasuwan magani dake karamar Hukumar Kajuru.

A cikin waata sanawa da ta firo daga ofishin mataimakin gwamnan Barnabas Yusuf Bala, yau Jumma’a, an umarci hukumomin tsaro su bi umarnin sau da kafa wajen aiwatar da dokar. Yayinda aka kuma yi kira ga al’ummar yankin su kiyaye dokar.

An dauki wannan matakin ne biyo bayan kashe wadansu mutane uku jiya da maraice da ake dauka a matsayin ramuwar gayya.

An yi fama da hare hare a karamar hukumar da ya yi sanadin kashe sama da mutane dari biyu tsakanin watan Oktoba shekara ta dubu biyu da goma sha takwas zuwa yau.

An bayyana karamar Hukumar Kajura a matsayin daya daga cikin sassan Najeriya da aka fi fama da matsalar tsaro.

A cikin sakon da aka wallafa a shafin sadarwar twitter na gwamnatin jihar ta ce dokar zata ci gaba da aiki har zuwa wani lokaci.

SECURITY UPDATE: The Kaduna State Government has imposed a 24-hour curfew in Kasuwan Magani with immediate effect. Deputy Governor Barnabas Yusuf Bala has directed vigorous enforcement of the curfew and has urged citizens to comply and support peace efforts in the community @GovKaduna

Ranar Jumma’ar da ta gabata ne wadansu ‘yan bindiga suka kai hari a wani wurin shakatawa dake Kajuru suka kashe ma’aikatan aikin jinkai biyu, Faye Mooney, wata ‘yar kasar Birtaniya da kuma dan Najeriya Ogwuche, a Nigerian.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG