A ci gaba da kai munanan farmaki da suke yi kan ‘yan ta'addan Boko Haram, sojojin Najeriya da Nijer wato rundunar sojoji ta musammnan ta 403 dake Baga, da takwarorinsu na Jamhuriyar Nijar, da kuma taimakon jiragen yakin Operation Lafiya dole sun afka wa maboyar mayakan Boko Haram dake kauyen Kure a zirin tafkin Chadi, inda bayan da suka kassara yan ta'addan sun kuma kwato motoci masu dauke da manyan makamai, da bindigogi da kuma sauran wasu makaman yaki.
Wannann na zuwa ne gabanin ganawa a game da tsaro da aka yi tsakanin Ministan tsaron Najeriya da takwaransa na Chadi a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya ranar Alhamis 9 ga watan Afirilu.
Wata sanarwa da ta fito daga daraktan sashen aikace-aikace a shelkwatar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Bernad Onyeaku, ta nuna cewa dakarun Bataliya ta uku, wato sojoji masu kai daukin gaggawa dake babban sansanin soji na goma sha daya a Gamboru, sun yi wata fafatawa mai zafi da ‘yan ta'addan.
A saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum