Kamfanin sada zumunci na WhatsApp ya fitar da sanarwar zai hakura da cajin mutane kudin da yake karba na shekara shekara. Cikin ‘yan shekarun baya ne WhatsApp ya sanar da cewa zai fara cajin sabbin masu amfani da shafinsa, bayan sun cika shekara guda ba tare da sun biya ko sisi ba.
A wata sanarwa da kamfanin yayi yace “Alokacin da muke habaka, mun gano cewa tsarinmu baya tafiya yadda ya kamata.”
Ya ci gaba da cewa, yawancin masu amfani da shafinmu basu da katin banki da ake kira credit card, kuma suna damuwa da ganin cewa ba zasu ci gaba da yin amfani da shafin ba wajen sada zuminci ga abokansu da ‘yan uwansu bayan sun cika shekara daya da fara amfani da shafin. Cikin makonni masu zuwa zamu fitar da cajin da muke, yadda ba za’a taba biyan kudi ba.
Ga mutanen da suka kwashe shekarau 6 suna amfani da WhatsApp, basu taba fuskantar biyan wannan kudi ba, domin dadewarsu kamfanin ya bar musu kyauta har tsawon rayuwarsu.
Yanzu haka dai kusan mutanen biliyan 1 ne ke amfani da WhatsApp a duniya, cire kudin da kamfanin ke caji zai kara wasu miliyoyin mutanen fara amfani da wannan shafi an sadarwa.