An ratsar da William Ruto a matsayin shugaban kasar Kenya bayan da ya samu nasarar lashe zaben da aka yi ta kai ruwa rana, ko da yake zaben ya gudana cikin Lumana.
Kimanin shugabannin kasashe 20 ne suka halarci bikin rantsar da shi a wani filin wasa na Nairobi mai kujeru 60,000, wanda ya cika makil da ’yan kallo kafin wayewar gari, yawancinsu sanye da riguna masu launin rawaya na jam’iyyar Ruto tare da daga tutocin Kenya.
Shahararren dan siyasa wanda ya kasance mataimakin shugaban kasa tun shekarar 2013, Ruto ya doke abokin hamayyarsa Raila Odinga - wanda shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta ke marawa baya - da kasa da kashi biyu cikin dari.
Yanzu haka yana shirin fuskantar wani gagarumin aiki na tafiyar da kasar mai fama da rarrabuwar kawuna da matsalar tsadar rayuwa da kuma fari mai tsanani, in ji manazarta.
Ruto mai shekaru 55 da haihuwa, ya taba sayar da kaji a bakin titi, yanzu kuma shi ne shugaban kasa na biyar a tarihin kasar Kenya tun bayan samun ‘yancin kai.