Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Kenya: Yadda Shari’ar Raila Odinga Za Ta Zama Zakaran Gwajin Dafi Ga Babbar Mai Shari’a Koome


Babbar Mai Shari'a a kasar Kenya, Martha Koome
Babbar Mai Shari'a a kasar Kenya, Martha Koome

Babbar jojin Kenya, Martha Koome da Shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta ya nada a watan Mayun 2021, ta yifice wajen nuna gaskiya. Ko yaya za ta kaya a shari'ar da shugaban 'yan adawa Raila Odinga ya shigar ta kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa?

Kenya, kasa ce da aka santa wajen katsalandan da ‘yan siyasa ke wa fannin shari’a, sai dai Martha Koome, babbar jojin kasar, mata ce da ba a yi wa shisshigi a al’amuranta na shari’a.

Sai dai jajircewarta wajen tabbatar da gaskiya na fuskantar kalubale bayan da shugaban ‘yan adawa Raila Odinga, ya shigar da kara yana kalubalantar sakamakon zabe shugaban kasa da aka yi a ranar 9 ga watan Agusta, wanda aka ayyana William Ruto a matsayin wanda ya lashe.

A watan Mayun 2021, Shugaba Uhuru Kenyatta mai barin gado ya nada Koome a matsayin babbar jojin kasar, wacce aka santa da tsage gaskiya.

Watannin bayan da aka nadata, ta yi watsi da wasu sauye-sauyen kundin tsarin mulki da Odinga da Kenyatta suka goyawa baya, wadanda ake musu kallon, yunkuri ne na rage tagomashin Ruto.

Bayan zaben 2017 ne Kenyatta da Ruto suka raba gari, inda shi Kenyatta ya hada kai da Odinga.

A halin da ake ciki, kan hukumar zaben kasar a rabe yake: shugaban hukumar kasar ya ayyana mataimakin shugaban kasa Ruto a matsayin wanda ya samu kusan kuri’u 233,000, sai dai hudu daga cikin kwamishinonin zabe bakwai, sun nuna adawa da wannan matsaya, inda suka ce an tafka kurakura wajen tattara sakamakon zaben.

Kungiyar farar hula mafi girma a Kenya, wacce ke sa ido kan zabuka, ta ce, kidayarta ta yi daidai da ta shugaban hukumar.

Duk wani kuskure da mai shari’a Koome ta yi wajen yanke hukunci a wannan shari’a, zai iya sa al’umar kasar su dawo daga rakiyar fannin shari’a kasar, wanda hakan, har ila yau, zai iya shafar mika mulki cikin ruwan sanyi a kasar ta Kenya, wacce ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a yankin gabashin Afirka.

Wannan takaddama, ta sa ana zaman dardar a kasar wacce ke da tarihin aukuwar munanan rikice-rikice da suka taba barkewa a lokutan zabe a baya.

“Muna kira ga fannin shari’ar da ya zama dan ba ruwanmu wajen yanke hukunci,” In ji wata kungiyar farar hula da ke kare hakkin bil Adama, inda ta kara da cewa, “zaman lafiyar kasar ya Dogara ne akan fannin na shari’a.”

Su kansu alkalan babbar kotun kasar ba su tsira ba, saboda a shekarar 2017 da kotun ta yanke hukunci kan sakamakon zaben 2017, an yi ta zagin su, inda har shugaban kasa ya ayyana su a matsayin “marasa gaskiya” aka kuma harbi wani mai tsaron kafiyarsu.

A shekarar 2017, kotun kolin kasar ta zamanto ta farko da ta soke nasarar da shugaban kasa mai-ci ya samu a zabe, bayan da ta yi watsi da sakamakon, lamarin da ya ba Kenyatta damar yin wa’adi na biyu. Kenyatta ya lashe zaben bayan da Odinga ya kauracewa zaben.

A halin da ake ciki, hudu daga cikin alkalan da suka yanke waccen shari’a, suna nan a kotun. Babban alkalin kasar ya yi ritaya, wanda Koome ta maye gurbinsa.

Koome, wacce ta kwashe shekaru 34 tana aikin shari’a, ta yi sunana ne kan yadda ta rika wakiltar ‘yan siyasar da aka tsare irinsu Odinga, a lokacin da ya jagoranci zanga-zanga a shekarun 1980 da 1990.

A wani hukunci da ta yanke a 2019, wanda ya sha banban da al’amuran kasar, Koome ta goyi bayan wani hukunci da ya nuna cewa bai laifi ba ne idan mutum ya ayyana kansa a matsayin dna luwadi ko madugo.

A kasar ta Kenya, hukuncin daurin shekaru ne 14 ga wanda aka kama da aikata wannan aiki.

Yayin wani taron yi wa kasa addu’a da aka yi a watan Mayun da ya gabata, Koome ta yi gargadi ga masu hawa tituna su ta da husuma idan ba su gamsu da sakamakon zabe ba

“Ina yi wa masu kwadayin ganin sun raba kan kasarmu addu’a, saboda wata bukata ta su. Wannan kasar, ta mu ce baki daya, ba ta ‘yan siyasa kadai ba.”

XS
SM
MD
LG