A lokacin da take gabatar da wani sabon kundin yaki da ta'addanci, Fatima Akilu ta ce ta yi tattaki har zuwa maiduguri da kanta, inda ta ganewa idanunta irin ci gaban da ake samu. Musamman ta yaba da goyon bayan da al'ummar jihohin Borno da Yobe da Adamawa suke bayarwa ga aiwatar da dokar-ta-baci.
Ta ce jama'a su na ta bayyana cewa tsinke hanyoyin sadarwa da aka yi, su na goyon bayansa ganin yadda ya taimaka wajen tumbuke 'yan bindiga daga sansanoninsu.
Ta ce ba za a iya wanzar da zaman lafiya cikin kwana guda ko wata guda ba, tilas abin zai dauki lokaci, amma kuma an fara ganin amfanin matakan da ake dauka.
Ta ce jami'an tsaro da sauran hukumomi su na daukar matakai masu yawa na tabbatar da cewa wannan fada da ake yi bai rutsa da fararen hula ba.
Sai dai har yanzu akwai wadanda suke ci gaba da kushe wadannan matakan da gwamnati take dauka. Dr. Umar Hardo, dan asalin Jihar Adamawa ne, wanda kuma yace babu ta yadda za a rika kashe wasu, sannan a juya a ce ana ceton rayuka.
Ga wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu el-Hikaya, da cikakken bayani.