Hajiya Mero Lawan ta yi jawabinta ne lokacin da ta kai kayan agaji da suka kai miliyoyin nera ma wasu kananan hukumomi.
Hajiya Mero tace matsalar hare-hare ta jefa jama'a da dama cikin mawuyacin hali yayin da mata da yawa suka rasa mazajensu kana yara kuma suka zama marayu. Tace Ubangijin da Ya haliccemu yana hakuri damu da irin halayenmu balantana dan Adam. Tace sabili da haka akwai bukatan wadannan mahara su yiwa Allah su hakura haka nan. Su kawo karshen matsalar da suka jefa jama'a.
Hajiya Mero yayi fatan Allah ya taba zuciyar 'yan kungiyar ya kuma tausayawa wadanda lamarin ya shafa.
Fanta Baba Shehu tsohuwar 'yar majalisar wakilan Najeriya ta kira iyaye mata da su dinga sa 'ya'yansu makarantu ganin yadda Mero Lawan ta sharewa mata hawaye a matsayinta na 'ya mace mai ilimi. Idan ba an ilimantu ba ba za'a iya gwagwarmayar taimakawa mutane ba. Sabili da haka 'ya mace ta yi karatu.
Wadanda suka anfana da tallafin sun yabawa Hajiya Mero wadda suka ce tafi namiji. Akwai maza da yawa basu yi komi ba amma ita ta tashi ta yi taimakon kayan agaji na miliyoyin nera.
Alhaji Muhammed Kogi ya kira wadanda aka dankawa alhakin raba kayan su yiwa Allah su tabbatar sun yi adalci. Ya kirasu su ji tsoron Allah.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu