Masana kiwon lafiya ciki har da Dr. Mohammed Ladan wanda yake amsa tambayoyin masu sauraro a Muriyar Amurka, sun ce na'urar zata taimaka sosai wajen sawwakawa masu karbar allurar ligakafi, sabo da wannan na'ura zata yi aiki ba tare da mai karbar jinya yaji zafin sukar allura a cikinsa ba. Musamman yara kanana.
Na'urar an taba amfani da wata shigenta shekaru masu yawan gaske da suka wuce, fasahar ce aka sabunta.
Haka kuma na'urar zata taimakawa masu fama da cutar sukari ko (Diabetes) wajen shawo kan radadi da suke samu wajen yiwa kansu allura.
Sai dai damuwar da ake da ita ahalin yanzu shine cewa na'urar bata yelwata ba, domin haka mallakarta yana da tsada. Kuma zai dauki dan lokaci kamin ya wadata ko ina. Ahalin yanzu fiye da shekaru 10 ana amfani da wannan na'ura anan Amurka.
Hukumar kula da magunguna da abinci ta Najeriya sai ta amince ta fara amfani da naurar kafin hukumomi da 'yan kasa su fara saye idan aka wanzar da ita.