Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kawo Karshen Taron G20 Da Tattauna Batutuwan Kasashen Kudancin Duniya


Shugabannin Duniya a taron kolin G20 a Rio de Janeiro
Shugabannin Duniya a taron kolin G20 a Rio de Janeiro

Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya sun kawo karshen taronsu na kwanaki biyu na G20 a Rio de Janeiro, tare da bayyana goyon bayan abubuwan da suka sa a gaba a kudancin duniya: sauyin yanayi da rage talauci da kuma sanya haraji kan masu kudi.

Baki daya ana daukar kudancin duniya a matsayin kasashe masu tasowa, ciki har da Rasha da kuma China.

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, mai masaukin baki a taron kolin G20, ya mayar da hankali kan tattaunawar muhimman ginshikai guda uku: hada kan al'umma da magance yunwa da fatara, sai makamashi da sauye-sauye kan ayyukan sauyin yanayi, da sake fasalin tsarin mulkin duniya.

A cikin sanarwar hadin gwiwa, kungiyar ta jaddada bukatar rage dumamar yanayi da rage talauci. Sun amince da yin aiki tare don “tabbatar da cewa ana karbar haraji daga mutane masu tarin dukiya.

Sanarwar ta ce karbar haraji “na daya daga cikin mahimman kayan aikin don rage rashin daidaito a cikin al’umma, habaka karfi, don tabbatar cimma burin Shirin Majalisar Dinkin Duniya na samar da ci gaba a duniya.

G20 ta sake yin kira da a fadada kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zuwa sama da kasashe biyar na dindindin da ake da su a yanzu.

Sakamakon aka cimma na nuna abubuwa masu ma’ana da gwamnatin Biden ta fi baiwa fifiko, in ji Matthew Goodman, darektan Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki ta Greenberg a Majalisar Harkokin Harkokin Waje.

“Amma babu masaniya kan ko nawa ne daga cikinsu za a ci gaba a gwamnatin Trump ta biyu,” in ji shi.

Za a rantsar da zababben shugaban kasar Donald Trump a watan Janairu. Wani babban jami'in gwamnatin Biden ya ce suna aiki don tabbatar da dorewar alkawurran Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG