Fitaccen dan siyasar mai farin jini sananne wajen sukar lamirin gwamnati, kuma shine wanda ya kafa wata jam'iyyar siyasa kasar da talakawa suke ji da ita.
Kisansa ya kara karfafa fushin jama'ar kasar kan gwamnatin Fara Minista Hun Sen, inda gungun mutane masu zanga zanga a harabar inda aka kashe shi suka hakikance, mutuwarsa shine mataki na baya bayan nan da gwamnati take dauka na tursasawa da matsin lamba kan 'yan hamayya da kungiyoyin fararen hula gabannin zaben kasar da za'a yi badi.
Kakakin rundunar 'yan sandan kasar ya ce tuni sun kama mutum daya wanda ya gayawa musu cewa shine ya harbe Ley, saboda yana binsa bashin dala dubu uku. Yace basu yarda da maganarsa ba, kuma ana ci gaba da bincike.