Yayinda kasashen duniya ke bukin ranar malamai ta duniya a yau 5, ga watan Oktoba, A Jamhuriyar Nijar gidauniyar tattalin iyali ta uwargidan shugaba Isuhu Mahamadu ta shirya wani buki domin karrama malaman da suka nuna kwazo akan aiki sai dai wasu kungioyin malaman kasar na ganin hukumomi na yiwa sha’anin ilimi rikon sakainar kashi.
Cikin yanayin annashuwa da raha aka gudanar da shagulgulan ranar malamai ta duniya wace kungiyar UNESCO ta kebe tun a 1994 domin karrama malaman makaranta da nuna mahimmancin a rayuwar Al'umma.
Taken ranar ta bana itace "Bukatar Maido Da Darajar Aikin Malanta"
Shugaban ma’aikatan a ofishin Ministan ilimi a matakin firamari Ashana Hima ya bayyana cewa hukumomi sun fara yunkurin soke aikin koyarwa a karksahin tsarin kwantaragi domin maye gurabe da tsarin cikakkun malaman makaranta da ake kira na dindindin.
Domin karawa malaman makaranta azamar aiki gidauniyar tattalin iyali ta uwargidan shugaban kasar Nijer Dr Malika Issoufou ta bayarda kyaututukan da suka hada da filayen gini babura kwamfitoti har da lambobin yabo ga malaman Jihohi 8 a Nijer. Kuma tayi kira garesu da su cigaba da wannan aiki na taimakon wajen ilimantar da Al’umma.
A ci gaban shagulgulan ranar malamai ta duniya shugaban kasar Nijer zai karbi bakunci wadanan malamai a yammacin wannan juma’a a fadarsa domin yi masu godiya saboda abinda aka kira rikon amanar da kasa ta ba su wato ilmantar da yara ilimi mai amfani.
Facebook Forum