Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Dan Birtaniya Da Niyyar Kashe Donald Trump


Donald Trump
Donald Trump

An cafke wani wani mutum dan Birtaniya a karshen makon da ya gabata a birnin Les Vegas, bayan wani yunkuri da jami’an tattara bayanan sirri su ka ce mutumin ya yi niyyar halaka dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyar Republican, Donald Trump.

Wani korafi da aka gabatar a ranar Litinin a wata kotun tarayya, ya nuna cewa Michael Steven Sandford, ya zo nan Amurka a makon da ya gabata, domin halartar taron gangamin Trump, inda ya yi yunkurin karbe bindigar wani dan sandan Las Vegas da ke baiwa Trump kariya domin ya harbe dantakarar.

Sandford ya yi ikrarin cewa, ya kwashe kusan shekara yana shirya kashe Trump, inda ya yi yunkurin aiwatar da kisan saboda ya samu kwarin gwiwar kashe dan takarar, kamar yadda wani jami’in tsaro ya rubuta a takardar korafin da aka gabatar a gaban kotun.

Ya zuwa yanzu ba a san dalilin da ya tunzura Sandford ya yi yunkurin kashe Trump ba.

Sandford ya gayawa hukumomi cewa bai taba harba bindiga a rayuwarsa ba, sai ranar juma’a da ya je wani wajen koyan harbi a Les Vegas.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG