Ofishin 'yan sandan jahar Pennsylvania ta kasar Amurka ta fitar da wani rahoto akan yadda wata mata ta farka daga bacci ta ga wani mutum wanda ya shigar mata gida ba tare da saninta ko izinin ta ba, kuma har ya wanke kayan sa kuma ya shiga cikin kwamin wankan ta yana wanka yana shakatawa.
Jami'an tsaron sun ce matar ta kira 'yan sanda zuwa gidan nata ne da ke a unguwar Greene Township kusa da inda ake kira Erie, ranar asabar da sassafe.
An caji Matashin dan shekarau 24 wanda ke zama a unguwar Orie mai suna James Shaffer da laifin shiga ba da izini ba, da nuna rashin hankali, da yawo cikin maye da yawon banza da kuma shiga da fita cikin dare.
A yanzu haka dai an garkame Shaffer a wani gidan yari da ke unguwar Erie har sai kotu ta yanke masa hukunci.