Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: An Kama Mota Cike da Takardun Zabe


Kama motar da ‘yan sanda suka yi a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ya haifar da ce-ce ku-ce da shakku a zukatan jama’a, tare da zargin yunkurin magudin zabe a babban zaben kasa mai zuwa.

Rundunar ‘yan sandan Jihar ta tabbatar da kama motar, inda kakakin rundunar D.S.P Lawan Abdullahi ya bayyana taka-mai-mai yadda lamarin ya faru.

“’Yan sandan mu wadanda suke kan sha-tale-tale, sune suka kama wata mota kirar ‘Golf’, motar nan akwai samfurin takardun zabe a ciki. An kuma kama matukin motar guda daya, to amma binciken mu ya nuna cewa wadannan takardu na zabe da aka samu, takardu ne na ilimantar da masu jefa kuri’a”, a cewar D.S.P Abdullahi.

Wannan yazo ne a lokacin da jama’a ke bude idanu da kunnuwa domin hana magudin zabe a babban zabe dake tafe a Najeriya. Wannan ba shine karo na farko da ake kama irin wannan mota ba, daga bisani a sake ta, ta kama gabanta.

A halin yanzu shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na yakin neman wa'adi na biyu a mulkin Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar PDP, sai dai tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya shine babban mai kalubalantar shi a karkashin jam'iyyar APC. Duk bangarorin sun dauki alwashin neman goyon bayan masoyansu domin tabbatar da zabe cikin kwanciyar hankali da walwala.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG