Ana jin jam'iyyar Fara Minista Rutte, zata sami kujeru 31 cikin kujeru 150 dake majalisar, wadda ya zarce na ko wace jam'iyya. Ana jin wasu jam'iyu uku zasu sami kujeru 19 a majalisa ciki harda jam'iyyar Wilders.
Jami'an zabe suka ce rabon da aga yawan jama'a da suka fito domin zabe haka tun shekaru 30 da suka wuce.Kashi 81 cikin dari na masu zabe ne suka fito.
Rutte ya kira sakamakon zaben "nasara ga tsarin demokuradiyya". Yace 'yan kasar Netherlands, sun ce fau-fau ga masu ra'ayin 'yan kishin kasa wanda ya kauce hanya."
Wilders,wanda irin zaton da ake masa a baya bayan nan na kasancewa babbar barazana ga Fara Minista,hakan bai tabbata ba, amma yayi kashedi ga Fara Ministan cewa "zasu sake karawa."
Shugabannin kasashen yammacin turai ciki harda ta Jamus, da Faransa da Luxemberg, duk sun bayyana murnarsu kan sakamakon zaben da taya Fara Minista Rutte murnar nasarar da ya samu.
Facebook Forum