Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: An Tsawaita Zabe Zuwa Lahadi


Kayan zaben 2015
Kayan zaben 2015

A Najeriya hukumar zaben kasar ta tsaiwata zabe zuwa gobe lahadi a wasu wurare bayan da aka samu tangardar na’urori da kuma matsalar tsaro.

Da safiyar yau akan samu rahotannin hare-hare a wasu yankunan jihar Gombe da Bauchi da tashin wani bam a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin yayin da aka kwance wasu bama-bamai da dama.

A hare-haren da akai, rahotanni sun ce an asarar rayuka da dan dama.

Najeriya dai na gudanar da zabukanta na shugaban kasa da na ‘yan majalisu a yau asabar.

Da yawa na kwatanta wannan zabe a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba saboda babban kalubalen da jam’iya mai mulki ta PDP ke fuskant a daga jam’iyar adawa ta APC.

Shugaba Goodluck Jonathan zai kara ne da Janar Muhammadu Buhari, wanda da ya taba mulkar kasar a lokacin mulkin soji.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG