Kungiyar rajin kare tattalin arzikin kasa da ganin an kimanta gaskiya, SERAP ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta saki shugaban hukumar cin hanci da rashawa Ibrahim Magu.
Kungiyar ta fadi hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a yau Talata mai taken "dole a yi wa Magu adalci."
SERAP ta jaddada cewa ya kamata a sami Magu da wani laifin kirki tukunna, idan ba haka ba a bashi damar tafiya gida.
Hakan na zuwa ne a dai-dai kwana daya bayan da ya fuskanci wani kwamiti wanda shugaba Buhari ya kafa domin wasu zarge-zargen da ake masa, masu alaka da aikinsa a hukumar EFCC.
Jaridar Premium times ta ruwaito cewa, kwamitin da Magu ya fuskanta ya tsare shi na sa'oi da dama, daga bisani aka kai shi wata cibiyar binciken 'yan sanda da ke area 10 a Abuja inda ya kwana.
A cewar sanarwar ta SERAP mai dauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, "SERAP ta umarci hukumomi da su baiwa Magu 'yancinsa na fuskantar shari'a yadda ya kamata."
Bayan da rahotanni da dama suka ruwaito cewa kama Magu aka yi a jiya, ita dai hukumar ta EFCC ta musanta hakan a cikin wata sanarwar da ta fitar, a cewar EFCC "gayyata ce kawai ya je amsawa."
Facebook Forum