Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana Fita Ba Dare Ba Rana A Yankunan Ibi Da Wukari Dake Taraba


Rahotanni daga kudancin jihar Taraba na cewa an samu wani tashin hankali a yankin Ibi, lamarin da yasa gwamnatin jihar kafa dokar ta baci, na hana fita na ba dare ba rana, sakamakon tashin hankalin.

Cikin kwanakin nan dai ana yawan samun harin sari ka noke a yankunan Ibi da Wukari, lamarin da yawancin lokuta kan koma fadan kabilanci ko na Addini.

A cewar wasu mazauna wannan yankin, suna ganin cewa wannan wani abune da a baya ake ganin kamar siyasa ce ke haddasa shi, to amma siyasar ta wuce kuma lamarin yaki ci yaki cinyewa, domin cikin garin Ibi da Wukari za a ga wani kabila ko wani Addini na hana wani bangare wucewa, haka kuma a jiya an kona wata mota da ta taho daga Ibi zuwa Wukari.

Yanzu haka dai an kara tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyar al’umma, DSP Joseph Kwaji, dake zama kakakin yan Sandan jihar ya gargadi al’ummar yankin da su shiga hankalinsu.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG