Koda yake masu magani basu tabbatarda wanan ba, masu amfani da wannan magani sun ce yawan masu mutuwa ya karu yayinda suka koma shan Tyonex, wanda ya shiga kasuwa a matsayin maganin cutar kanjamau.
Wani kamfani mai suna Tyonex Nigeria Limited wanda yake a Ikotun Egbe, Lagos, shine mai hada maganin kuma anyi ta tambayoyi da yawa game da ingancin maganin da kuma rashin sa shi cikin kwali mai nagari.
Koda yake an kawas da Tyonex daga kasuwa, wannan yanayi ya kawo maganganu masu yawa daga ma’aikatan lafiya, sauran jama’a da kuma mutanen dake dauke da kwayar cutar.
Yanzu Nijeriya ita ce ta biyu cikin kasashen da suka fi yawan masu cutar kanjamau a duniya. Duk da sa hannum da gwamnatin Nigeriya ta yi da PEPFAR domin taimakawa gwamnatin yaki da cutar kanjamau, har ya zuwa yau, samun maganin cutar ya zama matsala ga wadanda ke dauke da cutar a Nigeriya.