Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hallaka Wasu ‘Yan Bindiga Da Suka Kai Hari A Kaduna


Nigerian Air-force
Nigerian Air-force

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jiragen yakinta sun hallaka ‘yan bindigar da suka kai hari a wasu garuruwa dake karamar hukumar Igabi.

Babban hafsan hafsoshin rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ne ya bayyana cewa jiragen yakin rundunar sun kai farmaki kan ‘yan bindigar kuma sun dakile su daga kai duk wasu hare-hare a nan gaba.

Shi ma kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bada tabbacin cewa jiragen yakin saman Najeriya sun samu nasarar murkushe ‘yan bindigar. Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar Kaduna ba zata shiga wani sulhu da ‘yan ta’addan ba.

Wani tsohon babban hafsa a rundunar sojin Najeriya, Manjo janar Junaidu Sani Bindabawa, shi ma ya goyi bayan gwamnatin jihar Kaduna akan cewa sulhu da ‘yan ta’dda ba daidai ba ne.

A na sa ra'ayin, kakakin gwamnan jihar Katsina Abdu Labaran Malumfashi, ya ce, sulhu da ‘yan bindiga a jihar Katsina ya yi tasiri.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG