WASHINGTON, D.C —
Wannan yaro dai shine a matsayi na uku wanda zai gaji gidan sarautar Ingila.
Firayim Ministan Britania David Cameron ya fito gaban gida na goma a layin Downing, wato fadar gwamnatin Britaniya kennan, ya taya yarima Williams tare da mai dakinshi, mai jego Kate Middleton murnar wannan karuwa.
Firayim Ministan yace: Wannan labari ne mai dadin gaske daga asibitin St. Mary’s, kuma wannan labari ne mai dadin gaske ga al-ummar Britaniya da sauran kasashen dake karkashin ikon Britaniya. Kuma na tabbata duka al-ummar wadannan kasashe da mu al-ummar Britaniya zamu yi bukukuwa domin nuna jin dadin mu ga wannan babbar rana.
Haka kuma akwai sanarwar da ta fita daga kakan jaririn da aka haifa, wato yarima Charles, mai jiran gadon sarautar Ingila, kuma shine mahaifin yarima Williams.
Yarima Charles ya kara da cewa: Da ni da mai dakina, muna matukar farin ciki da jin wannan kyak-kyawar labari. Kuma wannan babbar rana ce ga mai jego, uwar jariri, wato Kate Middleton tare da maigidanta, Yarima Williams.