Rundunar sojojin saman Najeriya ta gargadi jami'anta da su guji yin katsalandan a harkokin zaben kasar da za a gudanar kwanannan.
Da yake magana a wani taron da ya gudanar da manyan kwamandojinsa, Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Sojojin Saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar, ya ce ba su da alaka da siyasa ko wata Jam'iyyar Siyasa.
Ya ce Babban abin da ya sha masu kai shi ne tababar da tsaron kasa da kare mutuncinta, don haka ya gargadi jami'an rundunar da su nesanta kansu daga shiga cikin harkokin siyasa.
Abubakar ya ce babu wata rawa ta kai tsaya da sojoji za su taka wurin samar da tsaro yayin zaben in ba bukatar hakan ta taso ba.
Ya kara da cewa za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana ko da 'yan sanda za su nemi taimakonsu wurin tabbatar da tsaro.
Babban Hafsan Hafsoshin sojin saman ya ce manyan jiragensu da ma Helikwaptocinsu za su zauna cikin shirin tallafawa hukumar zabe da jigilar kayayyakin zabe in aka nemi su taimaka.