Al'ummomin yankin tsakiyar Najeriya ko Middle Belt, sun koka kan abun da suka kira sakaci da hukumomi ke yi na rashin daukan kwararan matakan da zasu tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Yankin tsakiyar Najeriya da ake kira Middle Belt ya hada da kananan kabilu a jihohin arewa ta tsakiya da wasu bangarorin jihohin arewa maso gabashi da arewa maso yammaci.
Yankin ya sha fama da tashin hankali da ya yi sanadin salwantar dubban rayuka da dukiyoyi lamarin da ya saka al'ummomin yankin cikin tsoro da fargaba saboda abun da ka iya faruwa.
Farfesa Yusuf Turaki, ya ce daukacin al'ummar yankin na fuskantar matsaloli dake bukatar matakan gaggawa. Ya ce mutanen yankin sun sha fuskantar hasarar rayuka. Wadanda suke kashe kashen suna da makamai wadanda kuma ake kashewa basu da makamai. Injish bayan sun kashe mutane sai su mamaye wuraren mutanen da suka kashe dalili ke nan da mutanen yankin ke cewa yakin na kwace masu kasa ne. Ya kira gwamnatin tarayya ta tashi tsaye ta kare mutuncin kowane dan Najeriya.
Shugaban kungiyar raya kabilar Irigwe Sunday Audu, ya ce abun mamaki wurin da ake kashe kashe adaf yake da babban barikin soja na Bassa amma babu soja ko daya da ya tashi ya tsawata. Yana mai cewa Najeriya ba ta wani ba ne. Babu yadda za'a ce za'a kawar da kirista ko musulmi a kasar.
Shugaban al'ummar Fulani dake shiyar arewa ta tsakiya Danladi Ciroma, yace su ma makiyaya suna bukatar kariya. A cewarsa ya na gayawa makiyaya su zauna da manoma lafiya amma sojojin da aka kai jihar Binuwai sun hana Fulani sakat wadanda kuma haifaffun Binuwai ne kaka da kakanni.
A nasa bangaren, kakakin rundunar sojojin dake wanzar da zaman lafiya a jihar Filato Manjo Adam Umar, ya ce jami'an su na iyakar kokarinsu kan gudanar da aikinsu ba tare da nuna banbanci ba, saboda dakarun sojoji sun kunshi kabilun Najeriya daban daban.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum